Sojojin bayar da agajin gaggawa na gudankar da aikin su a yankin Ache na kasar Indonesia

Deutsche Welle, 03 January 2005

This article is available in German (including the radio interview) and also in Haussa language:

deutsche-welleHar yanzu ana fama da matsaloli a kauyen Aceh na yankin Sumatra a kasar indonesia, wajen gannin kayan bada agaji sun sami zuwa ga masu bukata a yankin.

Rashin kayan aiki da hanyoyi sun hana gudanar da shrin bada agajin ya tafi ndai-dai kamar yadda aka tsara a sauran bangarori da wannan balai ya shafa.

Anan nan ana fama da matsalar rashin hanyoyin shiga cikin sauran kauyukan yankin da wannan masaifa ta fadawa. Kayan agajin da a yanzu haka ake saukewa a filin jirgin saman Banda Aceh suna nan babu halin mika su ga mabukata. Kawo izuwa wannan lokaci, kayan aikin da kasar ta Indonesia take dashi kamar su manyan motoci da jiragen helikopter da wayoyin tarho sun kasance kakashin hukumar sojin kasar dangane da yakin basasar da kasar take fama dashi.

Ana da kwana daya da afkuwar wannan balai a yankin, shugaban hukumar sojin kasar ta Indonesia, janar Endriartono Sutarto, yayi kira na game da tsagaita wuta a tsakani da yan kungiyar GAM masu adawa da gwamantin kasar. Ita dai wannan kungiyar ta GAM ta dade tun daga shekarar 1976 tana kokarin neman yancin kann yankin Aceh mai albarkar kasa. Kuma tun daga shekarar dubu biyu da uku yankin na Aceh ya kasance yana cikin halin cikakken yaki, yakin kuma da kawo izuwa yanzu ya salwantar da rayukan mutane kimanin dubu goma sha-biyu a yanzu haka. Tun kafin wannan amabilayar ruwa ta sami yankin, dakarun gwamnatin kasar ta Indonesiakimanin dubu hamsin sunyi kakagida a yankin.

To sai dai kuma, kamar yadda jaridar Jakarta post ta ruwaito, ta sanar da cewar ba duka dakarun gwamnatin bane suke bada tasu gudunmawa a halin kakka-nakayi da kasar take ciki a halin yanzu. Wasu daga cikinsu suna cigaba da yakar yan kungiyar tawaye ta GAM, tare da bada hujja ta yakar masifu biyu a lokaci guda. A wani bangaren kuma, wasu daga cikin sojojin kasar suna bada tasu gudunmawar ga maiakatan bada agaji na kasashen duniya da suka isa kasar Indonesia domin taimakawa.

Jim kada bnayan da wannan balai na amabaliyar ruwa ya sauka akasar, sabon shugaban kasar ta Indonesia,Bambang Yudhoyono, yayi kira ga yan tawayen dasu ajiye makaman su a gefe, su koma tebirin shawarwari domin samar da wani tsari tabbabace da zai kawo karshen wannan yaki a kasar. A ranar 28 ga watan disamba daya gabata, gwamnatin kasar ta Indonesia ta kafa dokar ta baci a kasar, wanda samun hakan ya baiwa masu basda agaji na duniya damar shiga cikin kasar domin taimakawa waddanda wannan masifa ta fadawa hatta ma yankin yan tawayen.

Hakazalika kuma, harma da yan jarida sun sami damar shiga ba tare da wasu tsauraran kaidoji ba, domin su bayar da rahotanni a game da yankin na aceh. To sai dai kuma, da alamun wasu daga cikin sojin basu da labarin wannan sassauci da ya samu daga bangaren hukumar kasar. Duk kuwa da wannan rashin sani dake tattatare dasu, halin da aka shiga a yankin ya canza abubuwa da dama.

Kamar dai yadda wani wakilin kungiyar kula da hakkin dan adam ta watch indonesia ya sanar, wato alex flor, yace, yana ganin afkuwar tsunami a kasar ta Indonesia ta sanyayar da jikatan bangarorin biyu a game da yakin da suke da juna, wato dai wannan balai ne daga Allah, tsira kuma sai daga allah. To sai dai kuma, ba a da tabbas din cewar wanna hali zai cigaba da kasancewa a nan gaba a kasar. Hakan kuwa na da wuya ganin irin zaman da sojojin kasashen duniya zasu cigaba da yi a kasar domin bada gajai, wanda zai hana bangarorin biyu zu cigaba da tsaungwamar juna anan gaba.

Sha,awanatu Shehu


Tags: , , , , , , , ,


Share

Action!


Rainforest Instead of Palm Oil



Petitions

Follow us